Alkallumar na zuwa ne adai-dai lokacin da jakaden MDD a Yeman Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya gana a Aden da Abedrabbo Mansour Hadi kan dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta da lafar da kurar rikicin siyasar da ya taka rawa a yakin basasan kasar na shekaru biyu.
Saudiya ta shiga yakin Yemen ne a shekarar 2015 lokacin da Tsohon shugaba hadi ya gudu zuwa kasarta.
Kakkakin MDD Farhan Haq ya ce yawan rayukan da suka salwata ya nuna bukatar gaggauta komawa teburin sulhu, yayin da fararren hula ke ci gaba da neman bukatar agaji.
Sai dai Mansour Hadi ya yi watsi da daftarin da Ould Cheikh Ahmed jakaden MDD a Yeman ya gabatar na yiwuwar cim-ma zaman lafiya a kasar da ‘yan Husi.
Daftarin ya bukaci samar da gwamantin hadin-kai da ficewar ‘yan Husi daga birane kasar.
Mansour Hadi na gani cewa amincewa da bukatar ta MDD a matsayin Sulhu zai disashe karfinsa da bai wa mataimakinsa Fifiko.
Yakin basasan Yemen ya kasance daya daga cikin mafi muni da ya tagayara al’umma a duniya a cewar MDD.288
17 Janairu 2017 - 15:28
Lambar labari: 805538
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 10 Saudiya ta kashe a Yemen, tun lokacin da ta shiga yakin kasar don marawaTsohon Shugaba Abedrabbo Mansour.